Shugabar Ma’aikata, Winifred Oyo-Ita, ta ce sai da gargadi Shugaba Buhari kan dawo da Abdulrasheed Maina.
Maina wanda hukumar EFCC ke nema ruwa ajallo a kan zargin zamba cikin aminci, an dawo das hi bakin aiki ne cikin wani lamari mai cike da ruxani
A wata wasika da Jaridar Punch ta samo, Oyo-Ita ta ce ta yi wa shugaban kasa magana kan al’amarin a ranar 11 gawatan Oktoba, inda ta tabbatar mishi da cewa akwai matsaloli da dama da yin haka zai janyo.
Wasikar ta nuna cewa, Oyo-Ita ta gana da shugaban kasa a ranar Laraba 11 ga watan Oktoba bayan taron Majalisar Zantarwa “Inda na yi wa mai girma shugaban kasa bayani kan matsalolin da dawo Maina bakin aiki zai iya haifar wa idan aka dawo da Maina bakin aiki.”
Shi kuma Ibrahim Magu, shugaban Hukumar EFCC a ranar Litnin da gabata ya ce mutanen da suke kare Maina sun sa kama shi ya yi wahala.