✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na gamsu da yadda ake gudanar da zabe a Gombe —Makaman Cham

Ya bayyana cewar komai na tafiya yadda ake so a rumfunan zabe a jihar.

Dan Takarar Majalisar Wakilan Tarayya na Jam’iyyar PDP a mazabar Billiri da Balanga a Jihar Gombe, Ali Isa JC, ya nuna gamsuwarsa bisa yadda zabe ke gudana a jihar.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a mazabarsa jim kadan bayan kada kuri’arsa.

Ya ce ma’aikatan zaben da masu jefa kuri’a ba su samu wata matsala ba sai dai a wasu wurare da aka samu matsalar amfani da na’urar BVAS, amma daga baya aka shawo kan matsalar.

JC, ya yaba wa INEC kan inganta harkar zabe fiye da 2019 wanda ya ce yana fatan a zabe na gaba a sake samun ci gaba fiye da yanzu.

“Babu fargaba na rashin fitowa zabe tsakanin mata da maza; kowa ya fito kuma zabe na tafiya yadda ake so,” in ji shi.

Ali Isa JC, shi ne Makaman Cham, sannan ya taba zama dan majalisar wakilai na mazabar Billiri da Balanga a jam’iyyar PDP a 2015.