✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na fi sha’awar fitowa a matsayin boss a fim – Ibrahim Meku

Aminiya ta zanta da wani matashin dan wasan Hausa, wanda tauraronsa ke haskawa musamman a bangaren boss ko ta’addanci a finafinan Hausa, inda ya bayyana…

Aminiya ta zanta da wani matashin dan wasan Hausa, wanda tauraronsa ke haskawa musamman a bangaren boss ko ta’addanci a finafinan Hausa, inda ya bayyana yadda ya tsinci kansa a cikin harkar fim da sauransu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ka gabatar da kanka ga masu karatu?

Sunan Ibrahim Abubakakar, amma a harkar fim an fi sani na da Ibrahim Meku. An haifeni a wata Unguwa da ake kira Gama da ke yankin Birged a karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano. Na yi makarantar firamare a Gama Tudu special primary school, sannan na yi sakandaren gwamnati ta Gobernment Commercial da ke kan titin filin jirgin sama, inda na kammala a shekarar 2000. Daga nan sai Allah Ya yi na dawo Kaduna wajen kanwar mahaifiyata da ke zaune a unguwar Hayin Banki, inda a nan ne na samu damar ci gaba da karatu har zuwa matakin N.C.E.

Me ya ja hankalinka ka shiga harkar fim?

Gaskiya na kasance ma’abocin kallon finafinan Hausa tun ina karami. Irinsu Garinmu da zafi, Tumbin Giwa, Bakan Gizo, da sauransu. Gwanaye a lokacin su ne kasimu Yero, Bashir Nayaya, Kabiru Barmo, Ibrahim Mandawari da sauransu. To saboda shauki, nima kawai sai na shiga harkar. Kuma na fara harkar fim din ne a shekarar 2007.

Finananka sun kai nawa yanzu?

Gaskiya na yi finafinai da dama da ba zan iya kayyadewa ba, amma sai dai wanda aka fara ganeni shi ne Garinmu da zafi, wanda ya hada fitattun ’yan wasa kamar Adam Zango, da Ali Nuhu da Zainab Indomie da Maryam Both, inda na fito a mai tsaron Adam Zango. Sai dai kuma finanfinan da suka fi shahara a wadanda na fito su ne Gwaska, Andamali, Wuta Sallau, Babbar Yarinya, Nas, da sauranzu.

Wane bangare ka fi sha’awa ka fito?

Dariya! Gaskiya na fi sha’awa na fito a bangaren da aka saba ganina, wato a matsayin Boss, ko ince ta’addanci, amma fa a fim kawai. Saboda shi fim shiryawa ake yi, kuma yadda ya zo, haka za ka yi. Kawai ana dubawa ne aga wanda zai dace da sakon da ake so a isar zuwa ga al’umma domin su fahimci sakon da kyau.

Ko kana da wani uban gida a harkar fim?

Duk wani babba da ke masana’antar Kannywood daga masu tsarawa finafinai, masu shiryawa, da ’yan wasan duk iyayen gidana ne, domin akwai kyakkyawar fahimta a tsakanina da su. Sai dai wanda na fi kusanci da shi, shi ne mai gidana Adam A. Zango. Domin a yanzu haka, wasu idan suka ce Meku, sai sun kara da Zango a gaba saboda kusanci. Ke nan akwai kusanci mai karfi.

Ko kana da wata kira zuwa ga ’yan fim ’yan uwanka?

Ina kira ga sauran jarumai ’yan uwana da duk wanda ke masana’antar Kannywood da mu ji tsoron Allah a duk al’amuran da muke yi, domin mun riga mun zama madubi a cikin al’umma. Dole mu siffantu da alamomin fadakarwa kamar kyakkyawar ma’amala, shigar kamala da sauransu, musamman ma jarumai mata domin su ne aka fi magana a kansu, har ake samun damar fada mana maganganu. Da fatar za mu gyara.

Ko kana da kira zuwa ga masu sha’awar kallon finafinaku?

Ina kira ga masoya harkar fim da cewa muna godiya matuka da soyayyar da suke nuna mana. Allah Ya bar zumunci. Kuma muna bukatar shawarwari a duk lokacin da kuka ci karo da kuskuren daya daga cikinmu. Sannan kuma ku rika yin kira ta hanyar da ta dace domin mu taru mu gyara baki daya. Mun gode. Sannan ina godiya ta musamman ga Jaridar Aminiya da ta bani wannan dama. Allah Ya kara daukaka.