✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na fi fitowa a bangaren soyayya da matan aure a fim – Ahmad Muhammad

Aminiya:  Ka gabatar mana da kanka? Sunana Ahmad Muhammad mai kamfanin shirya fina-finan Hausa na kmedia da ke Jihar Kano. Aminiya: Me ya ja hankalinka…

Aminiya:  Ka gabatar mana da kanka?

Sunana Ahmad Muhammad mai kamfanin shirya fina-finan Hausa na kmedia da ke Jihar Kano.

Aminiya: Me ya ja hankalinka ka shiga harkar fina-finan Hausa?

To ni gaskiya Alhamdulillahi ba wani ne ya kawo ni ba, dama can ina da ra’ayi kuma  ni na kai kaina .

Aminiya: Ta wane mataki ka fara fim tunda kace ba karkashin wani ka fara ba kuma ba wani ya jawo ka ba?

Gaskiya ba ina shigowa na fara fina-finai ba sai da da danyi wasu ayyuka da wasu mutane tukuna kafin daga baya sai na ga nima ai ya kamata in shigo domin in bayar da ta wa gudunmawar, tunda kowa yana da irin nasa tunanin na daban. Shi ne nake ganin nima in bayar da nawa tunanin inda nake ganin ya fi dacewa, shi ne na fara shirya fina-finai.

Aminiya: Kafin ka fara shirya fim naka, ko zaka iya fada mana sunayen wasu daga fina-finan da ka yi?

Gaskiya bazan iya tuna adadin fina-finan da na yi ba, don gaskiya suna da yawa kuma na taka rawa iri-iri amma akwai wadanda na fi taka muhimmiyar rawa a cikin su.

Aminiya: Kamar wadanne ke nan?

Gaskiya na fi taka rawa a bangaren soyayya!kuma nakan fito a soyayya da matan aure ne a fim.

Aminiya: Wannan rawa da kace kana takawa a fim ko ka taba fuskantar wani kalubale ko tsangwama daga masu kallon fina-finan, ganin cewa kana soyayya da matan aure domin wasu sukan fuskanci irin wannan matsalar?

To gaskiya ni dai ban taba fuskantar kalubale irin wannan ba sai dai dan abin da ba za a rasa ba. Sai dai wani abu dana fuskanta da zan iya kiran sa kalubale kamar irin haka shi ne wasu mata da muke karatu da su a makaranta ban san wasu ba amma na san suna tsokanata, amma dai na san cewa tsokana ce kawai suke min. Wasu ko da gaske suke yi ko ba da  gaske ba, su dai suka sani, gaskiya kuma sai Allah da ya yi su, amman abin da nasan nakan fuskanta ke nan kawai.

Aminiya: Kai ne Shehu Miji a fim din maza da mata inda ka  sace jakar da maigida ya zo da ita wadda ake zaton akwai dalar Amurka a ciki, lamarin da ya jefa matar gida cikin matsala tsakaninta da mijinta mene ne hikmar hakan?

Gaskiya ne nine na fito a cikin wannan fim din na maza da mata da suna  Shehu Miji. Kuma duk rigimar fim din ma idan ka duba za ka ga akai na ake yi. Ita Rahama ta kasance matar aure, ni kuma mun hadu a makaranta kawai sai muka fara soyayya da ita har ma ta nemi in rika koya mata karatu, muna dai dan yin haka muna badda kama, to mun yi da ita zanzo gidan in kwana domin in koya mata karatu, ina zuwa gidan da na yi sallama na ji ba a amsa ba, alamun bata nan tunda dama na saba zuwa gidan ni kuma na ga jaka a falonta da daloli a ciki kawai na yi awon gaba da ita na yi tafiyata. Ita ma bata san na dauka ba sai daga karshe ta sha wahala ni ma na sha wahala a kotu.

Aminiya: Banda wadannan fina-finan akwai wasu da kake yin aiki a kan su yanzu?

 Akwai wasu fina-finai guda 3. Akwai ga mace ga namiji da mutuncin ‘ya mace, akwai kuma sama ta kasa.

Aminiya: Mai karatun zai so sanin manufar fim din mutuncin ‘ya mace, wane darasi zai koyar?

To wannan labari gaskiya zai koyar da darussa iri-iri, kadan daga cikin su ne  Al’umma ta gurbace da yawan tallace-tallace. Mace ko iyayen suna da hali ko basu da shi  ya kamata ace ta yi karatu, karatun kuma kowane iri ne domin shi zai taimaka mata shi zai bata damar tarbiyyartar da ‘ya’yanta da kuma al’ummar da Allah Ya hada ta dasu a gaba tunda dama tarbiyya a hannun mata take. Wannan fim mutuncin ‘ya mace labari ne da yake magana a kan ainihin rayuwar mata da kuma yadda suka tsinci kan su, domin ya fi kyau ace suna da ilmi, su rika zuwa makaranta wannan ilmi shi ne zai rika taimakawa rayuwarsu. A takaice wanna shi ne dan takaitaccen bayani a kan fim din mutuncin ‘ya mace.

Aminiya: Wane matsayi ka fitowa a fim din domin makarantan mu su gane kai ne idan fim din ya fito?

A fim na fitowa inda nake soyayya da wata matar aure.

Aminiya: A fina-finan da kake shiryaw kana fitowa cikin su ko kuwa sai dai ka sanya wasu su fito?

 A’a, gaskiya bana fitowa a ciki.

Aminiya: Wasu jama’a na yi wa ‘yan fim zargin masu bata tarbiyya ne wasu kuma suna ganin cewa ba haka abin yake ba, ya kake ganin lamarin?

 To kasan kowa da irin tasa fahimta. Ance fahimta fuska, na san a gaskiya akwai irin wadannan maganganun amma ni gaskiya ban fuskanci irin wannna kalubalen ba domin yawancin mutane mu suke fuskanta. Tunda ni gaskiya ba boyayye bane, na yi karatu don ban ma fara harkar fim ba sai da na sauke Alkur’ani  sannan kuma karatun Boko har yanzu ina yi. Mafiya yawancin mutane masu kallona a fim sun riga sun san ko waye ni  sun san abin da zanyi sun san wanda ba zan yi ba to gaskiya ban fuskanci wannan kalubalen ba .

Aminiya: Gashi kun zo Jihar Kuros Riba aiki, yayin da wasu kuma ke kyuyar zuwa ya kuka samu al’umma musamman ‘yan arewa mazauna kurmi?

 Gaskiya bamu fuskanci wata barazana ba  da muka zo nan. Mun ga yadda ‘yan uwa ‘yan Arewa mazauna Kalaba suka karbe mu hannu bibbiyu, kuma mun gode.  Allah Ya bar zumunci.