Tsohon Ministan Sufuri kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Rotimi Amaechi, ya ce yana da gogewar zama shugaban kasar Najeriya a 2023.
Amaechi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da daliget jam’iyyar APC a Makurdi, babban birnin Jihar Benuwe.
Ya roki daliget din jam’iyyar su zabe shi a zaben fid da gwani da ke tafe, a matsayinsa na dan takara wanda ya fi kowa cancanta, gogewa da gaskiya.
“Ni ne wanda ya fi kowa gogewa a cikin masu neman takarar Shugaban Kasa a APC da PDP, na yi Shugaban Majalisa shekara takwas, na yi Gwamna shekara takwas, na yi Minista na shekara bakwai.
“Na san yadda ake tafiyar da al’amura a lokacin da na yi Minista, na zagaya kasar nan, sannan kuma na zama shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya lokacin da na zama Gwamna.
“Akwai lokacin da Shugaban Kasa na wancan lokacin ya kira ni ya ce mun mayar da Kungiyar Gwamnoni zuwa kungiyar kwadago.
“Ni ne dan Najeriya na farko da ya cire gwamnati mai ci da jam’iyya mai mulki daga kan karagar mulki,” inji shi.