Fitaccen malami addinin Islama, Sheikh Ahmed Gumi, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba ya kaunar Najeriya kamar yadda yake yi.
Gumi ya bayyana hakan ne yayin da yake martani dangane da kama Tukur Mamu da Hukumar Tsaro ta DSS ta yi.
- Zaben 2023: Atiku da Tinubu da Kwankwanso da Obi a sikeli
- Dalibai sun daure malami sun lakada masa duka kan samun maki kadan
Sheikh Gumi wanda ya yi wannan furuci a karatunsa na mako-mako da ya saba gabatarwa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, ya ce an cafke Mamu ne saboda rawar da yake takawa ta shiga tsakani wajen sakin wadanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.
A cewarsa, doka ta tanadi cewa ana gurfanar da duk wanda ake zargi a gaban kuliya bayan sa’a 24 da kama shi.
“Allah Yana jarabtar muminai, kuma wannan wata hanya ce ta jarrabawa daga Allah a kan Mamu.
“Ku kai shi kotu ya fuskanci shari’a don tsare shi a gidan yari ba tare da an bayyana laifinsa ba abun damuwa ne kwarai da gaske.
“Wannan lamari akwai firgici a cikinsa kuma ta’addanci ne. Kama mutane bisa zalunci, shi ma ta’addanci ne; kamar yadda ’yan ta’addan ke yi ta hanyar zuwa gidan mutane su sace su kuma su yi garkuwa da su.
“Ta ya za a yi mu ci gaba da rayuwa a irin wannan yanayi a karkashin gwamnatin da wa’adinta ya zo karshe?
“Babban fatanmu shi ne gwamnatin ta gama lafiya.
“Kuma ba wai don Tukur Mamu aka kama ba, kun san cewa duk wanda aka kama bisa zalunci sai na fito na yi magana, ballantana kuma a kama wanda na sani.
“Ina mai shawartar gwamnatin da ta gaggauta sakinsa kuma ta nemi yafiyarsa komai ya zama tarihi,” a cewar Sheikh Gumi.
“A matsayinmu na wadanda suka san abin da ya kamata, ba za mu iya nade hannayenmu mu zauna haka kawai ba. Na san yadda wadannan ayyukan tsaro suke kasancewa saboda ni kaina ina cikin tsarin.
“Na san yadda ake ayyukan kuma na san duk wata kitumurmura da ake kullawa.
“Ko Sardauna bai tsira ba a lokacinsa, haka Murtala da Maimalari da IBB da shi kansa Buharin. Dukkansu sun dandana irin wannan tuggu
“A kwanan nan Malam Goni ya sake fada wa tarkon wannan tuggu yayin da wasu kananan sojoji suka kashe shi.
“Ni da kaina na dauki matakin kwantar da hankalin ’yan bindiga domin a samu zaman lafiya a kasar nan, sai dai duk da hakan wadansu ba sa son gaskiya.
“Bari in gaya muku ko Shugaban Kasa ba ya kaunar kasar nan kamar yadda nake yi domin ba ni da wata kasa sai Najeriya.
“Ina son a samu zaman lafiya da aminci a kasar wanda hakan ya sa na yi kasadar shiga daji domin a magance matsalar tsaro.
“Amma akwai wadanda ba sa son a samu zaman lafiya. Ba su da burin ganin an magance matsalar tsaron da ta addabi kasar.
“Saboda sun gano cewa na dauki lamarin da muhimmanci, sai suka soma kira na da sunaye iri-iri suna alakanta ni da ta’addanci
“Abin da ya fi bata min rai shi ne lokacin da na ba da shawarar cewa wadannan mutane [fulani makiyaya da ake kira ’yan bindiga] suna bukatar ababen more rayuwa kamar asibitoci da makarantu kamar yadda aka tanadar wa tsagerun Neja Delta, sai aka bige da zagi na,” a cewar Sheikh Gumi.
Yadda Tukur Mamu ya shiga hannu
A makon da ya gabata ne jami’an ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol suka kame Tukur Mamu a Masar lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Umara a kasar Saudiyya, dalilin da ya sanya dawo da shi Najeriya don amsa tambayoyi daga jami’an tsaro.
Tukur Mamu wanda shi ne kakakin Sheikh Gumi, shi ke matsayin mai shiga tsakanin don sakin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su tun cikin watan Maris din shekarar nan.
Hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta sanar da samun tarin kakin Soji da makudan kudade a gida da ofishin Tukur Mamu yayin sumamen da suka kai masa.
Gano wadannan kayaki na zuwa ne bayan kame Tukur Mamu mawallafin jaridar Desert Herald a Larabar da ta gabata, lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano.