Al’ummar Nahuche a Jihar Zamfara sun yi zanga-zangar neman gwamnati ta gaggauta tsaurara matakan tasro a yankinssu, bayan sun kashe Naira miliyan 100 wajen biyan kudin fansa ga ’yan bindiga, amma da su daina kai musu hari ba.
Sun gudanar da zanga-zangar ce a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara kan yadda hare-haren ’yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudaden fansa suke faru a kusan kowace rana a tsawon shekakara uku.
- ’Yan bindiga sun kai harin daukar fansa kan mayakan Boko Haram a Kaduna
- Buhari ga sojoji: Ku hanzarta murkushe ’yan bindigar Neja
Da yake jagorantar zanga-zangar, tsohon Shugaban Hukumar Bungudu, Musa Abdullahi Manager, ya ce, “Yanzu shekara uku ke nan da ake kawo wadannan hare-hare ana garkuwa da mutanenmu; Mun kashe kimanin Naira miliyan 100 domin biyan kudin fansa da daukar nauyin ’yan sa-kai, amma har yanzu ba a daina kawo hari ba.
“’Yan bindiga sun kutsa cikin yankin sun sace mutane sun karbi kudin fansa Naira miliyan biyar, amma suka ki sakin mutanen, cewa sai an kara musu da sabbin babura guda biyu.
“Ana cikin tattaunawa da su kuma suka sake zuwa suka sace wasu mutum takwas, suna neman wani kudin fansar,
“Yanzu haka mutanen Nahuche 13 ne a hunnunsu, muna rokon gwamnati ta ceto su,” inji shi.
Ya ce ko a baya-bayan nan ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan kasuwa, Alhaji Hadi Babban Gebe, suka karbi kudin fansa Naira miliyan 35, sannan suka kashe shi.
“Mutane sai kaura suke ta yi daga garin saboda hare-haren, duk kuwa da irin makudan kudaden da mazauna suke kashewa domin samar da tsaro, saboda mun dauki ’yan sa-kai da yawa aiki.
“Mun yaba da da kokarin gwamnatin jiha da ta tarayya wajen yaki da matsalar rashin tsaro, amma al’amarin garin Nahuche na bukatar daukatar tsauraran matakai, saboda haka muke so a girke jami’an tsaro a garinmu, idan ba haka ba, nan gaba za a wayi gari kusan duk mutanen garin za su tashi,” kamar yadda ya bayayan.
Samun Kakaikin ’Yan Sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, domin jin ta bakinsa ya ci tura, har muka kammala hada wannan rahoto.