Ministar Jinkai, Agajin da Cigaban Jama’a, Sadiya Farouq, ta ce hankalin ma’aikatar ya karkarta zuwa daukar matasan da za su ci gajiyar shirin N-Power rukuni na uku.
Sadiya ta ce a halin yanzu babu wani matashin da ke bin ma’aikatar bashin ko kwabo daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin N-Power a rukunin A da B.
“Mun warware dukkanin basukan alawus na N-Power tare da Ofishin Akanta-Janar na Tarayya; yanzu mun mayar da hankali kan daukar rukuni na uku,” inji Ministar.
Da take magana ranar Laraba a wata bita ga ’yan jarida, Sadiya ta ce ofishin Akanta-Janar na Tarayya ya biya alawus-alawus din matasan da ma sauran basukan alawus din da ake bin ma’aikatar.
Idan za a iya tunawa wadansu da suka ci gajiyar rukunin B na shirin sun yi ikirarin cewa suna bin ma’aikatar alawus na N30,000 wanda gwamnatin ke biyan ’yan N-Power.