Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin N-Power rukunin “C”, wanda sabbin matasa miliyan daya za su amfana a karkashinsa.
Da take kaddamar da kashin farko na sabbin matasan a Abuja, Ministar Agaji da Kyautata Rayuwa, Sadiya Umar Farouq, ta ce an kasa rukunin na “C” zuwa gida biyu.
- An yanke wa jarumar Kannywood hukuncin komawa Islamiyya
- Majalisar Zamfara ta daina zama bayan garkuwa da mahaifin shugabanta
Ministar ta ce, “Kashin farko (C1) za a dauki matasa 510,000, a rukuni na biyu (C2) kuma matasa 490,000.
“A C1 akwai gurabu 450,000 domin matasa da suka kammala karatun digirin farko su amfana, sai kuma matasa 60,000 marasa shaidar kammala karatun digirin farko.”
Sadiya ta kara da cewa an bullo da sabbin tsare-tsare domin ganin shirin na N-Power ya tafi cikin sauki.
“Domin magance matsalolin intanet da kuma isa ga dukkan wadanda suka cancanta, Ma’aikatarmu ta yanke shawarar amfani da lambar USSD domin samun bayanai.
“Mun tanadi lambar USSD ta *45665# domin samar da bayanan da suka dace ga masu bukata daga cikin matasan da za su ci gajiyar shirin,” inji ministar.
Sauran shirye-shiryen sun hada da kafa Hukumar Kula da Ayyukan Kyautata Rayuwa da kuma yin hadin gwiwa da hukumomin da suka dace domin saukaka samar da bayanai domin aiwatar da shirin da kuma biyan matasan hakkokinsu.
Ta ce shirin na N-Power yana da bangarori uku kamar haka:
- ‘N-Power Volunteer Corps’, domin matasa da suka kammala digirin farko.
- ‘N-Power Build’ na matasa wadanda ba su da digirin farko.
- ‘N-Power Knowledge’ na marasa digirin farko amma an kebe shi ne domin bayar da horo a kan fasahar sadawar zamani da gyaran kwamfuta da dangoginsu.
A karkashin shirin za a rika biyan matasa masu digiri N30,000 a duk wata na tsawon shekara daya, sauran kuma za rika biyan su N10,000 a duk wata na tsawon wata tara.
An kirkiro shirin ne domin rage zaman kashe wando da samar wa matasa ayyukan yi da kuma kawar da hankulansu daga aikata miyagun ayyuka.