✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muzaharar Ashura: An kashe mana mutum 6 a Zariya — ’Yan Shi’a

Sun kuma yi zargin jami'an tsaro sun jikkata wasu da dama

Kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN) ta mabiya Shi’a ta yi zargin cewa jami’an tsaro sun kashe mata mambobi guda shida yayin muzaharar ranar Ashura ta bana a Zariyan jihar Kaduna.

Kungiyar ta kuma ce an jikkata mata mutane da dama.

A zantawarsa da wakilanmu a Zariya, jagoran kungiyar, Abdulhamid Bello, ya yi zargin cewa wani ayarin jami’an tsaro ne ya yi wa tawagar tasu dirar mikiya a daidai lokacin da suke kokarin kammala muzaharar a kusa da kasuwar birnin Zariya, inda suka rika harbinsu.

Ya ce mutanen da aka kashe sun hada da Jafar Magaji Jushi da Kazeem Lawal Magume da Ali Lawal Samaru da Muhsin Badamasi Yakub Zakzaky da Umar Inuwa Anguwar Fatika da kuma wani mutum da ba su kai ga tantance sunansa ba.

Abdulhamid Bello ya kuma ce har yanzu ba su san adadin mutanen da aka jikkata musu ba, sakamakon an garzaya da su asibitin St. Luke da ke unguwar Wusasa, yayin da wadanda ke cikin mawuyacin hali kuma aka kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce sun sami rahoton arangamar, amma ya ce zai yi masa karin bayani daga bisani.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai kai ga yin hakan ba.