Mutuwar fitaccen marubuci Ustaz Aliyu Umar Chiromawa wani lamari ne da ya samar da wani babban gibi a fagen rubutun Hausa da na addini a duniyar adabi, don kuwa in ka duba yadda ya bada gudunmawa a harkar tun shekaru masu yawa, to lallai abin a dade ne ana tunawa da shi, saboda zaunannen abu ne abin da ya yada na ilimi za a ci gaba da cin gajiyarsa har karshen rayuwa.
Shi dai Ustaz Aliyu Umar Chiromawa wanda Allah Ya yi wa rasuwa da yammacin ranar Juma’a 20 ga watan Fabarairu, 2015 bayan wata gajeriyar rashin lafiya, mutum ne da duniya ta sanshi a fannin rubutun addini da kuma karantarwa tsawon rayuwarsa har ya koma ga Allah yana da shekara 65.
Littafinsa na farko da ya rubuta a 1981 shi ne ‘Isra’i Da Mi’iraji’ na Hausa, littafin ya samu karbuwar da babu wani littafin Hausa da ya kai shi karbuwa, domin kuwa duk wata makarantar Islamiyya da ke kasar Hausa tun daga wannan lokacin tana amfani da shi har zuwa yanzu.
Bayan shi akwai fitattun littattafan marubucin kamar: ‘Bushara’ da ‘Makircin Shaidan’ da ‘Alamomin Tashin Alkiyama’ da kuma ‘Rayuwar Annabi (SAW) wadanda ake amfani da su a makarantun Islamiyya a kasar Hausa.
Marigayin ya kasance marubucin Hausa da ya fi kowa yawan littattafai da aka wallafa, domin kamar yadda ya tabbatar kafin rasuwarsa bai san yawan littafin da ya rubuta ba, abin da aka fi sani shi ne, tun a 1999, ya yi bikin cikar rubuta littafinsa na 100, kuma daga wancan lokacin zuwa rasuwarsa ya rubuta sama da 150, kuma a rubutunsa babu wani bangare da bai taba ba, domin duk wani al’amari na rayuwa babu inda bai taba ba.
Ya yi rubutu a kan fassarar mafarki da tarihin Annabawa da tarihin sahabbai da tarihin bayin Allah magabata, kuma har annoba da take faruwa lokaci zuwa lokaci Malam yakan yi rubutu a kanta shi ne ya zamo jagoran kafa kasuwar littattafan addini na Hausa a kasuwar Kurmi, wadda ta yi bunkasar da ake zuwa daga kasashen Afirka domin sayen littattafan.
Baya ga haka marigayin gwarzo ne wajen yada addini, ya kasance karatu da karantarwa kamar a jininsa yake don kuwa a tsawon rayuwarsa abin da ya gudanar ke nan.
Ya bada gudunmawa a fannin da ba za su misaltu ba, domin kuwa ya kafa makaranta Islamiyya sun fi 50 a tsawon rayuwarsa, ya kuma bude majalisai da dama na tafsirin Alkur’ani ga daliban makarantunsa da suke samun ilimi.
Hakika wannan bawan Allah ya kafa tarihin da duk mutum nagari zai so ya samu irin wannan damar ta hidima ga addini, kuma ya rasu a ranar Juma’a babbar rana da yamma bayan ya yi sallar Juma’a kuma ’yan mintuna bayan ya idar da sallar La’asar. Allah Ya jikansa Ya kyautata makwancinsa, Ya inganta zuri’arsa, amin.