Huduba ta Farko:
Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya halicci sammai ba tare da wasu turaku da kuke ganinsu ba. Godiya ta tabbata ga Allah, kuma Shi ne Ma’ishi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata bisa BawanSa da Ya zaba, Annabinmu Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da wanda ya jibince shi. Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya hukunta mutuwa a kan bayinSa, kuma Ya kadaita da rayuwa da tabbata.
Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma sai magagin mutuwa ta zo da gaskiya.” Kuma Madaukaki Ya sake cewa: “Kowace rai mai dandanar mutuwa ce, kuma wallahi za Mu jarrabe ku da alheri da sharri a matsayin fitina, kuma gare Mu ake mayar da ku.”
Bayan haka, ku ji tsoron Allah ya ku Musulmi matukar jin tsoronSa! Ku yi riko da igiyar Musulunci mai aminci, ku sani lallai ne Shi (Allah) Ya tserar da ku daga wuta. Kuma lallai mala’ikan mutuwa ya kauda kai ne daga gare ku ya koma ga wasunku, kuma da sannu zai bar wasunku ya komo gare ku, don haka ku zauna cikin shiri! Mai hankali shi ne wanda yake taka-tsantsan da ransa kuma yake yin aiki domin abin da ke zuwa a bayan mutuwa. Kasasshe shi ne wanda ya bi son zuciyarsa, kuma ya rika gurace-gurace a kan Allah.
Ya ku Musulmi! Lallai mafi girman wa’azi shi ne mutuwa, wadda Allah Ya kaddara ta a kan wanda Ya so daga cikin halittu. Komai nisan ajalinsa da tsawon rayuwarsa sai mutuwa ta riske shi, ya mika wuya ga karfinta. Allah Madaukaki Ya ce: “Kowace rai mai dandanar mutuwa ce, sannan zuwa gare mu ake mayar da ku.” (Ankabut:59).
Da Allah zai sanya dauwamma ga wani daga cikin halittunsa da ya kasance annabawanSa masu tsarki da manzanninSa mukarrabai ne. Kuma da wanda zai fi su cancantar haka shi ne zababbe daga cikin zababbunSa (Annabi Muhammad (SAW), amma hakan bai yiwu ba, sai ma Ya shaida masa cewa: “Lallai ne kai mai mutuwa ne, kuma lallai su ma masu mutuwa ne.” (Zumar:30).
Mutuwa tilas ne babu makawa daga gare ta, kuma ba a guje mata, za ta riske mu a cikin gidajenmu da kan duwatsu da sararin sama da karkashin ruwa. Mala’ikun da ke cikin sama ma ba su tsere mata, haka mala’ikun da ke kasa. Babu wani mutum ko aljani ko dabba da zai tsere mata, koda ta kasancewa a cikin gidajen masu tsaro da dogayen katanga, “Duk inda kuka kasance mutuwa za ta riske ku, koda kuna cikin gidaje masu tsaro.”
Da ana kubuta daga mutuwa da mutum ya ba da jikinsa da karfinsa da dukiyarsa da wadatarsa da iko ko mulkinsa da abin da ya mallaka domin ya kubuta daga gare ta. Abin ya yi girma ga mutane ba su hankalta. Idan ba haka ba, ina Adawa da Samudawa? Ko ina Fir’auna ma’abucin turaku? Ina Kisrori da kaisarori? Ina manyan jabbaran masu mulki? Mutuwa ba ta jin tsoron kowa kuma ba ta barin kowa. Tana dauke jariri daga bakin nonon uwarsa. Tana auka wa matashi saurayi ko mai karfi da jarumtaka ta yi galaba a kansa.
Ya ku mutane! Sha’anin mutuwa a bayyane yake kuma a fili. Gurbinta sirri ne daga cikin asirrai wadanda suke zama abin lura ga masu hankali. Ta girgiza tare da shan kan hankulan mutane, ta bar masana falsafa da likitoci suna ta kai-kawo cikin rudu ba su gano sirrinta ba. Tsayawa bincike a kan mutuwa bata ce mabayyaniya da bala’i mai girma. Babu mai mantawa da ita face ya yi dagawa, babu mai gafala daga gare ta face tababbe, kuma ita ba ta da magani. Ba a kauce mata, sai dai mutum ya rika tuna fadin Allah Madaukaki: “Rai bai san abin da zai aikata gobe ba, kuma bai san a wace kasa zai mutu ba. Lallai ne Allah Masani ne Mai ba da labari.” (Lukman:30).
Za mu cigaba insha Allah