✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutumin da yake sayar wa da ’yan bindiga babura ya shiga hannu a Kano

Na sayar wa da ’yan bindigar akalla babura 100 a kan farashi mai tsoka.

’Yan sanda sun cafke wani mutum da ake zargi yana sama wa ’yan bindiga baburan da suke kai hare-hare a Jihar Zamfara.

Rahoton da shafin BBC Hausa ya ruwaito ya ce mutumin wanda aka kama a Jihar Kano, bayanai sun nuna cewa yana sayen baburan sannan ya kai wa ’yan bindigar a Jihar Zamfara inda suke saye a kan farashi mai yawan gaske.

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce mutumin da aka kama ya shaida musu cewa ya sayar wa da ’yan bindigar akalla babura dari a kan farashin da ya haura naira dubu dari shida duk daya.

DSP Kiyawa ya ce bayanan sirri da suka tattaro a wurin wadanda mutumin yake sayen baburan a wurinsu a Jihar Knao sune suka taimaka wajen samun nasarar damke shi.

Ya ce mutumi ya kan shigo Kano daga Zamfara inda bayan ya sayi baburan sai ya sake komawa Zamfara domin ya kai wa ’yan bindigar su kulla cinikayyarsu.

“Babur yake sayarwa kirar Honda ACE 125, wanda ake kiransa da Boko Haram a can jihar Zamfara, wanda gwamnatin jihar tuni ta hana amfani da shi.”

“Idan suka zo jihar Kano sai su saya su sauya musu kwali, a hake suke shigar da shi daji, inda a can ake hada shi sannan su yi amfani da shi wajen kai wa mutane hare-hare,” in ji DSP Kiyawa.

Ya kara da cewa, sun kama mutumin ne da Babura guda biyu, wanda har an sauya musu kwali za a fitar da su daga Jihar Kano zuwa Zamfara.

Sau tari mutanen gari musamman a Jihohin da hare-haren ’yan bindiga suka yi kamari na Jihar Katsina da Zamfara, sun bayar da shaidar cewa ana kai musu hari ne a kan babura, lamarin da ya sanya gwamnatin jihar Zamfara ta dauki matakin haramta amfani da wasu daga irin wadannan babura don tabbatar da tsaro.