Rahotanni daga Iran sun tabbatar da mutuwar Amou Haji da aka ce shi ne uban masu dauda na duniya.
Kafar yada labaran yankin ta ce, a ranar Lahadi Haji ya rasu a kauyen Dezhgah, inda ya bar duniya yana da shekara 94.
- Gasar Kofin Duniya: Sarkin Qatar ya koka da sukar da kasar ke sha
- DAGA LARABA: Yadda Masu Aure Suka Zama Mazinata A Najeriya
Kafar ta ce, a halin rayuwarsa marigayin ya shafe shekara 60 ba tare da wanka ba, wanda ake zargin hakan ya yi silar rashin lafiyar da ya yi fama da shi.
An ce a tsakanin ’yan watannin da suka gabata mazauna kauyen suka matsa a kan sai marigayin ya yi wanka, inda suka dauke shi zuwa makewayi suka yi masa wanka, kamar yadda jaridar Telegraph ta rawaito.
Jaridar ta kara da cewa, bayan yi masa wanka ba da dadewa ba ya soma rashin lafiya wanda a Lahadin da ta gaba ta ya ce ga garinku nan.
Bayan rasuwar Haji, ana kyautata zaton wani dan kasar Indiya mai suna Kailash “Kalau” ne ya zama magajin Amou Haji, wanda aka ce rabonsa da wanka tun a 2009.