Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta gurfanar da wani mutum mai shekaru 47 a gaban wata Kotun Majistare bisa zarginsa da satar wani injin hada Burodi.
Tun da fari dai dan sanda mai gabatar da kara, S.A Adegbesin ya bayyana wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a shekarar 2018 a unguwar Egbeda da ke jihar.
Ya ce wanda ake zargin ya sace injin sarrafa burodin ne da ya kai darajar Naira miliyan hudu, mallakin wani kamfani mai suna Global Concepts.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta zargin aikata laifin wanda mai shigar da karar ya ce ya saba wa sashi na 309 da na 411 na Kundin Manyan Laifukan Jihar.
Mai shari’ar da ta jagoranci zaman kotun, A.O Akinde ta ba da belin wanda ake zargin kan Naira miliyan daya da sharadin gabatar da mutum daya wanda zai tsaya masa kuma ya mallaki makamantan kudin belin da aka nema ya biya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, mai shari’ar ta kuma dage zaman kotun zuwa ranar 22 ga watan Nuwamba.