✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutumin da ya gina masallacin matafiya na Kaduna ya rasu

Ya rasu ne a wani asibiti a Abuja ranar Laraba.

Attajirin nan da ya gina masallacin matafiyan nan da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya, Alhaji Sule Bako, ya rasu.

Aminiya ta gano cewa attajirin ya rasu ne a wani asibiti da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ranar Laraba, kuma an yi jana’izarsa a Kaduna da misalin karfe 1:09 na rana.

Ya rasu yana da shekara 84.

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan mamacin da ke kan titin Wushishi Road a Kaduna, ya iske dandazon masu ta’aziyya da suka je gaisuwa ga iyalansa.

Ya bar ’ya’ya 13 da jikoki da dama.

Daya daga cikin ’yan uwansa ya shaida wa Aminiya cewa marigayin ya bar gibin da cike shi zai yi matukar wahala.

Ya ce rasuwar babban rashi ce ga iyalansa, Jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya, inda ya ce marigayin ya yi rayuwa abar koyi.