Mutumin da ya fi kowa yawan shekaru a duniya ya rasu bayan shekara akalla 127.
Iyalan dattijon mai suna Natabay Tinsiew, wanda makiyayi ne daga kauyen Azefa na kasar Eritriya, sun ce an haife shi ne a shekarar 1894, kuma ya rasu ne a ranar Litinin 10 ga Oktoba, 2021.
Wani jikansa, mai suna Azefa Natabay, ya shaida wa Kundin Tarihi na Guiness da ke ba da lamba ga mutanen da suka kafa tarihi a duniya, cewa dattijon ya haura shekara 127 a duniya, don haka ya kamata a karrama shi a hukumance, bayan rasuwarsa.
Zere ya shaida kafar yada labarai ta BBC Tigrinya cewa iyalan sun gabatar wa Kundin Tarihin na Guiness takardun shaidar haihuwar dattijon daga wani coci da ke tabbatar da haihuwar dattijon a 1894.
A halin yanzu dai Kundin Tarihin Guiness na tantance ingancin takardun haihuwar da ke nuna tsohon ya shekara 127 a duniya.
Iyalan Natabay dai na ganin shekarunsa sun haura hakan, domin a cewarsu, sai da ya shekara kusan 10 a duniya kafin aka yi masa baftisma a coci a shekarar 1894.
A cewar Zere, sirrin tsawon kwanan kakansa Natabay Tinsiew a duniya shi ne hakuri da mutunci da kuma annashuwa.
Natabay dai ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da kuma garken shanu da awaki da dama.