✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 10 ina sata a masallatai —Ɗan shekara 74

Shekara 10 ina sata a masallatai, in ji dan shekara 74

Wani tsoho ɗan shekara 74 ya shiga hannu inda aka kama shi yana satar tabarmar masallaci a Jihar Kaduna.

Wannan tsoho dai ya amsa cewa ya shafe sama da shekaru 10 yana shiga masallatai ya sace tabarminsu.

Ya kara da cewa wani lokaci ma yakan saci agogon bangon masallatai, amma bai taɓa satar Alkur’ani ba.

An kama wannan tsoho yana satar tabarmin ne a wani ƙaramin masallaci da ke unguwar Rigasa a Karamar Hukumar Igabi.

Dubunsa ta cika ne a masallacin da ke layin Sarkin Bori Sule, a ranar Talata, bayan an addabi masallatan unguwar da satar sabbin tabarmi.

Mutumin ya kuma amsa cewa karo na biyu ke nan da ya saci tabarmi daga masallacin da aka kama shi.

Ya ce, “Da ni ake sallar jam’i, idan mutane suka fice sai in dauke sabbin tabarmi. Nakan sayar da kowacce a kan N1,500 zuwa N2,000.”