Afeez Agoro, mutumin da aka yi ittifakin ya fi kowa tsayi a fadin Najeriya, ya rasu.
A cikin tattaunawarta da Aminiya ta wayar salula, wata ’ya uwar marigayin da ba ta amince a ambaci sunanta ba, ita ce ta tabbatar da rasuwar.
- Sojoji sun lalata masana’antar kera bama-bamai ta ISWAP a Borno
- An kama Hakimi kan zargin yi wa yarinya mai shekara 5 fyade a Gombe
Ko da aka tambaye ta labarin dan uwan nata, sai ta fashe da kuka ta ce, “Ba ya nan, ya tafi. Ya riga mu gidan gaskiya, zan kira ka anjima,” sai ta katse wayar.
Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke Legas da yammacin Laraba, bayan ya sha fama da doguwar jinya.
Kafin rasuwarsa, Afeez yana da tsawon kafa bakwai da inci 11.
An haife shi a unguwar Sabo Yaba da ke Legas a matsayin da na uku kuma na karshe a wajen mahaifiyarsa, wacce kuma ita ce mata ta biyu a wajen mahaifin nasa.
Marigayin dai ya yi ta yin tsawon, sai da ya shekara 19, kafin ya fara fama da wata cuta da ake kira Acromegaly a Turance, wacce ke kara wa mutum tsayi fiye da kima.
Tun a lokacin dai ya yi kokarin magance ta domin ya tsaya a tsawon kafa bakwai da inci biyar, wanda duk da hakan, yana cikin mutanen da suka fi kowa tsayi a nahiyar Afirka.