Kimanin mutum 18 ne aka cafke tare da gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin karya dokar tsaftar muhalli garin a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a ranar Asabar bayan atisayen, Babban Jami’in Duba-Garin Jihar, Abubakar Mohammed, ya sanar da kotun cewa an kama wadanda ake zargin ne saboda yin watsi da aikin tsaftar muhalli inda suke gudanar da harkokin su a jihar.
- IPOB: An hallaka mutum 2 a hari kan ofishin ’yan sanda a Imo
- An kaddamar da mafarauta 1,000 don yaki da Boko Haram a Borno
“Mun kama akalla mutum 18 saboda karya dokar tsaftar muhalli a Nasarawa,” inji shi, kuma ya saba da sashe na 9 (2), na Dokar Tsaftar Muhalli ta jihar.
Mohammed ya kara da cewa kotun ba ta da wani zabi da ya wuce ta hukunta su domin hakan ya zama izina ga masu aikata laifi irin nasu.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Kasa na Jihar Nasarawa, Ibrahim Musa, ya ce nan ba da jimawa ba jihar za ta mayar da shara zuwa dukiya.
A cewarsa, Gwamnatin Tarayya a karkashin Ofishin Kula da Muhalli ta samar da wani tsari na sake sarrafa shara, kuma tsarin na dab da kammaluwa.
A cewarsa, “Nan ba da dadewa ba sharar za ta za ta yi karanci a cikin jihar saboda ana shirin sake yin amfani da duk abubuwan sharar gida tare da mayar da su dukiya.
“Mun riga mun samu wadanda za su rika sayen sharar, muna kira ga jama’a da su kasance masu bin doka tare da guje wa zuba shara a magudanan ruwa, saboda hakan ba abu ne mai kyau ba,” inji shi.
Ya kuma yaba wa al’ummar jihar saboda bin umarnin ma’aikatar wajen tabbatar da tsaftataccen muhalli don samun ingantacciyar lafiya a jihar.