✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum ɗaya ya mutu 4 sun jikkata bayan fashewar bam a Neja

"Mutane biyu da suka garzaya daga Bassa don yin agaji sun sake taka wani bam ɗin a kusa da wurin da yarana suke.  Abin takaici,…

Wani manomi ɗaya mai suna Dauda Haruna ya rasu yayin da wasu huɗu da suka haɗa da ‘yan’uwa 3 suka samu munanan raunuka bayan fashewar bam a unguwar Bassa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a tsakanin unguwannin Bassa da Gwadara a safiyar ranar Alhamis lokacin da waɗanda abin ya shafa za su tafi gona domin girbin amfanin gonakin su.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa, fashewar ta farko ta tashi ne da wasu ‘yan’uwa 3 da suka haɗa da: Mali  mai shekara 20 da Nehemiah  mai shekara 14 da Jona  mai shekara 15 da suka hau babur ɗaya yayin da na biyun ya tashi da babur na masu neman ceto ya taka, hakan ya kashe ɗaya daga cikin waɗanda suka je ceto, Dauda Haruna.

Mahaifin yaran 3, Mista Enoch wanda ya yi ta ƙokarin hana hawayensa ya shaida wa wakilinmu a Asibitin Ƙwararru na IBB da ke Minna inda ake jinyar waɗanda abin ya shafa, cewa wannan shi ne karo na biyu da bama-bamai suka tashi a cikin wannan watan a garin Bassa.

Mista Enoch ya ce yaran sun yi gaba ne a kan babur yayin da yake tafiya da matarsa ​​da ƙafa sai suka ji ƙara mai ƙarfi.

“Za mu yi noma ne don girbin amfanin gona, don haka na ce yarana su fara yin gaba a babur, ni da matata mu tafi a ƙafa, sun yi nisa da mu amma sai muka ji ƙara kamar harbin bindiga, muna cikin magana kamar cewa wai ‘yan fashi ne, wani ya zo daga waje ɗaya yanzu ya shaida mana cewa wasu yara sun taka bam. Na san ‘ya’yana ne.

“Mutane biyu da suka garzaya daga Bassa don yin agaji sun sake taka wani bam ɗin a kusa da wurin da yarana suke.  Abin takaici, ɗaya ya rasa ransa,” in ji shi.

Biyu daga cikin ‘yan’uwan Nehemiah da Jonah da ɗaya daga cikin waɗanda suka je ceto, Abdullahi Shuaibu sun rasa ƙafa ɗaya kowanne.

Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya yi alƙawarin gano yadda lamarin yake da yin martani, amma har zuwa lokacin haɗa rahoton bai yi ƙarin bayani ba.

Sai dai an yi ƙoƙarin kiran Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar Neja, Birgediya Bello Abdullahi Mohammed (RTD) kiran ya citura. Kuma bai amsa saƙon da aka aika a wayarsa ba.