Akalla mutum takwas ne mazauna ke fargabar sun mutu sakamakon gobarar gas da aka samu a Legas.
Masu aikin ceto sun tabbatar wa Aminiya cewa an fitar da gawarwawiki takwas baya ga wasu mutum uku da aka ceto.
Jami’in Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) Ibrahim Farinloye ya ce gobarar ta tashi ne a lokacin da “tankar mai ke sauke iskar gas a kamfanin Best Roof, inda janareto ke kunne, lamarin da ya haddasa tashin wuta.
“Bindigar ta gas din ta yi ta yi wurgi da motar da ke sauke iskar gas din a tsallake hanya.
“An gano gawarwaki biyar amma ana ci gabad da aiki yayin da gine-gine da dama suka kone”.
Shaidu sun ce ana fargabar mutane sun makale a cikin gine-ginen da gobarar ta kama baya ga wasu da dama da suka jikkata.
Gobarar ta kona gine-gine 25 ciki har da makaranta da gidaje da shaguna.
Gobarar gas din na kamfanin Best Roof da asubahin ranar Alhamis a yankin Alimosho, Jihar Legas na zuwa ne mako uku bayan an samu irinta a tashar iskar gas a yankin Iju/Ajuwon da ke tsakanin jihohin Legas da Ogun.