✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum shida sun warke daga cutar Coronavirus a Legas

An kara samun wadanda suka warke daga cutar Coronavirus a Legas. Mai taimakawa gwamnan Legas a kan sha’anin kiwon lafiya Dakta Tunde Ajayi ne ya…

An kara samun wadanda suka warke daga cutar Coronavirus a Legas.

Mai taimakawa gwamnan Legas a kan sha’anin kiwon lafiya Dakta Tunde Ajayi ne ya bayyana hakan, yana cewa mutum shidan da suka warke an yi jinyar su ne a Asibitin Kula da Masu Cututtuka Masu Yaduwa da ke Yaba.

Dakta Tunde Ajayi, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter @thetundeajai, ya ce za a sallame su nan ba da jimawa ba.

A baya ma mutum na farko da ya shigo da cutar Najeriya dan kasar Italiya ya warke a birnin Legas inda aka sallame shi a makon jiya.