Hukumar Asusun Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ta bayyana Najeriya a matsayin kasar da aka fi samun yawan mutanen da ke bahaya a bainar jama’a wadanda adadin su ya kai miliyan 46.
Jami’in hukumar, Sam Adejo Okedi ya ce duk da ci gaban da aka samu ’Yan Najeriya miliyan 46 ke bahaya a fili, matakin da ke barazana ga lafiyar jama’a a sassan kasar.
Alkaluman UNICEF da aka gabatar na kananan hukumomin Najeriya 774 sun nuna cewar a kananan hukumomi 10 ne kacal ba a samun masu bahaya a fili, wanda shi ne kashi 10 bisa 100 a Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewar an yi nasarar magance matsalar da ake samu na yawaitar masu bahaya a bainar jama’ar a Jihohin Jigawa da Katsina da kuma Binuwe.
Shugaban hukumar UNICEF da ke kula da shiyar Kano da Sakkwato, Maulid Warfa ya bayyana haka, inda ya danganta ci gaban da matakin da hukumomin yankunan ke dauka na magance matsalar.
Sashen Hausa na Rediyon Faransa ya ruwaito Warfa yana cewa an samu nasarar dakile wannan dabi’ar ce a kananan hukumomi 21 da ke Katsina da 18 a Jigawa da kuma guda 9 a Binuwe.
Jami’in ya ce kashi 25 na mutanen da ke zama a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na amfani da bayan gida wajen biyan bukatun su, yayin da kashi 35 kuma ke samun kula ta fannin tsafta.