✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum miliyan 30 za su rasa aikin yi idan aka hana acaba a Najeriya – Musa Maitakobi

Ya ce ya kamata a yi tunanin makomarsu kafin dakar matakin

A yi wa’yan acaba miliyan 30 da ake son raba su da sana’arsu tanadi – Musa Maitakobi

Yayin da wasu ’yan Najeriya ke goyon bayan Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da shirin kafa dokar hana sana’ar acaba kwata-kwata, matakin da suke ganin zai taimaka wajen kawo karshen matsalar tsaro, shi kuwa Shugaban kungiyar Masu Motocin Sufuri ta kasa (RTEAN) Alhaji Muhammed Musa Maitakobi cewa ya yi, yin dokar zai kara haifar da tabarbarewar tsaro. Ya fadi haka ne cikin hira da Aminiya.

Me za ka ce a kan kafa dokar hana adaba?

Wane tanadi aka yi wa masu aikin acaba su fiye da miliyan 30 a fadin kasar nan da ake son a raba su da aikin da suka dogara da shi wajen samun abinci a irin wannan lokaci na kuncin rayuwa? Idan Gwamnati ta yi masu tanadi na kwarai da zai maye gurbin sana’arsu ba tare da tsoma hannun masu yin zagon-kasa ga ayyukan ci gaban kasa ba to babu laifi a kafa irin wannan doka.

Amma muddin ba a tanadar masu abin yi ba to kuwa ina ganin za a samu karuwar tabarbarewar tsaro ne a kasa a maimakon shawo kan lamarin domin miliyoyin ’yan acaban da aka raba su da aiki suna iya shiga sahun bara-gurbin mutane wajen ci gaba da aikata miyagun ayyuka.

Ana zargin cewa akwai da yawa daga cikin ’yan acaba da suka shigo daga wasu kasashen Afrika da suke hada baki da ’yan Najeriya wajen aikata miyagun ayyuka. Ba ka ganin yin dokar zai taimaka wajen dakile ayyukan nasu?

Ya kamata a yi nazarin komai a tsanake saboda guje wa fadawa cikin wata matsalar da ta zarce wacce ake ciki. A matsayin gwamnatin kasa me zai hana daukar matakan binciken kwakwaf ga dukkan masu aikin acaba domin gano ainihin baragurbin ’yan kasashen ketare daga cikin su. Babu jami’an tsaro a cikin kasar ne? Ni dai nawa ra’ayi da shawara ita ce kada a kuskura a yi dokar hana acaba ba tare da tanadi ga masu wannan aiki ba.

Idan aka yi doka a kan mutane (‘yan ta’adda) da yawansu bai wuce miliyan daya ba da zai hana mutane fiye da miliyan 30 yin aikin dogaro da kai to ka ga an-yi-ba-a-yi-ba kenan, domin wadannan miliyan 30 da aka hana su cin abinci babu wata mafita gare su da ya wuce shiga kowane irin aiki domin samun abin sawa a bakin salati.

Kwanan baya rundunar tsaro ta Amotekun a wasu Jihohi na Kudu maso Yamma ta kama matafiya ’yan Arewa fiye da dubu daya cunkushe cikin manyan motoci amma sai motoci da suka fito da sunan yawon ci-rani a wannan sashe. Wace hanya kake ganin za a iya yin maganin aukuwar irin haka a nan gaba?

Da farko ni dai ban ga laifin irin wadannan matafiya ba domin mafi yawanci sun baro garuruwan su ne domin tsira da rayukansu a dalilin damun su da kai da hare -haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka raba su da matsuguni da dukiya da rayuka. Irin wadannan mutane sun rasa abin yi a wuraren da suke zaune, saboda haka suke rububin zuwa wannan sashe domin samun tsira.

Daya daga cikin hanyar magance wannan matsala ita ce gwamnatocin jihohin Arewa da attajirai masu hannu da shuni da Sarakuna da dukkan masu fada aji su yi amfani da dukiyarsu tsakani da Allah wajen samar da guraben ayyuka da tallafin jarin kudi ga wadannan matasa domin gudanar da kananan sana’o’i da nake ganin yin haka ne kadai mafita.

Amma muddin hakan bai samu ba, to babu wata hanyar da za ka iya hana irin wadannan mutane ficewa daga yankunan su domin neman abin da za su ci.