Mutum daya ya mutu yayin da masu aikin ceto na kokarin hako sauran mutum uku da benen da suke zaune a ciki ya rushe da su da tsakar dare a yankin Legas Island na jihar Legas.
Jami’in hukumar agaji ta kasa (NEMA) na yankin Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye, ya ce mutum goma ne suka makale a ginin mai hawa uku wanda ya rushe da misalin karfe uku na dare, a layin Freeman.
“An yi nasarar ceto mutum shida daga cikinsu a raye, sannan ana ci gaba da kokarin kubutar da sauran”, yana mai cewa dukkan wadanda ake ceto din manya ne.
NEMA, da hukumar agaji ta jihar Legas (LASEMA) da sauran masu aikin ceto na aiki kan jiki karfi wajen harkar baraguzan ginin domin ganin an hako mutanen.
Zuwa yanzu babu bayani game da musabbabin rushewar ginin da ya rutsa mutanen.
Amma ana yawan samun rushewar gine-gine musamman benaye a jihar Legas, wadanda yawanci ake dora alhakin a kan rashin ingancinsu.