✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum dubu 300 suka nemi aikin gurabe 4000 a FRSC

Hukumar Kare afkuwar hadurra ta Najeriya FRSC ta tantance akalla matasa dubu 324 wadanda suke neman aiki a gurabe 4,000 na hukumar. A yayin da…

Hukumar Kare afkuwar hadurra ta Najeriya FRSC ta tantance akalla matasa dubu 324 wadanda suke neman aiki a gurabe 4,000 na hukumar.

A yayin da shugaban hukumar FRSC Dakta Boboye Oyeyemi ya kai ziyara harabar da ake tantancewar a Abuja ya ce, hukumar nada guraben ma’aikata 4,000 ne kacal ga wadanda suka yi nasara.

Oyeyemi ya ce, za a tantance masu neman aikin na matakai daban-daban tun daga shaidar kammala karatun mai neman aikin da jarabawar gwaji wanda hukumar shirya jarrabawa shiga jami’o’i JAMB  ta shirya da kuma tantancewar ko mai neman aikin na yin mu’amala da miyagun kwayoyi.