✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daya daga cikin wadanda karya ta ciza ya sake mutuwa a Kano

A satin da ya wuce ne dai karyar ta ciji mutum biyar a Kano.

An sake samun wani mutum daya da ya mutu bayan cizon wata mahaukaciyar karya a unguwar Kofar Dan Agundi da ke birnin Kano.

Abbas Abubakar ne wanda ya sake rasuwa, bayan jinya da ya sha fama da ita a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) da ke Kano a sanadin cizon karyar.

Dan uwansa mai suna Abubakar Ibrahim Abubakar ya shaida wa manema labarai cewar “Ya kira ni ne da Asuba ya ce min ya kwana bai yi barci ba, numfashinsa yana daddaukewa. To kuma kafin na zo ake fada min numfashin irin wani yaro da kare ya cije su tare ,  yake yi, shi ne mahaifiyarsa ta ke tambayarsa yaushe kare ya cije su bai fada ba.

“Shi ne ya ce ai an kai wajen wata biyu da faruwar lamarin,” cewar dan uwansa.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce wata mahaukaciyar karya ta hallaka wani matashi mai suna Faruk Usman bayan ta  gantsara masa cizo da wasu abokansa su hudu a jihar.

Dan uwan marigayin da ya yi jinyarsa, Saddiku Usman, ya ce mutum guda daga cikin abokan yana kwance a asibiti, sauran kuma suna karbar magani.

Yanzu wanda ke jinyar a asibiti shi ma ya ce ga garinku nan sanadin cizon mahaukaciyar karyar.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce akalla mutane 55,000 ne ke mutuwa kowace shekara sakamakon kamuwa da cutar cizon mahaukacin kare da sauran cututtuka masu alaka da hakan da ke yaduwa da kashi 99 cikin 100.

WHO ta ce rashin bai wa cutar muhimmaci da al’umma ke yi ne ya sanya adadin ke kara karuwa duk shekara a Najeriya.