✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum biyu sun shiga hannu kan safarar makamai a hanyar Zariya

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu nasarar kama wasu mutane biyu da zargin safarar makamai. Kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan ne…

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu nasarar kama wasu mutane biyu da zargin safarar makamai.

Kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan ne ya bayyana haka a yayin da yake yi wa manema labarai holen ababen zargin a shalkwatar rundunar da ke Kaduna.

Mutanen biyu da aka kama — Zubairu Musa mai shekaru 40 da Nasiru Saidu mai shekaru 17 — dukkansu mazauna garin Kankara da ke Jihar Katsina.

ASP Hassan ya ce an kama su ne a kan hanyar Zariya zuwa Jos a lokacin da jami’an kwantar da tarzoma da ke Zariya suke gudanar da sintiri kan hanyar sakamakon bayanen sirri da suka samu akan ababen zargin.

A lokacin binciken an sami bindigogi ƙirar gida 8 sai ƙaramar bindiga ɗaya da kuma ƙwanson harsasai 65.

ASP Mansur Hassan ya ci gaba da bayanin cewa dukkan waɗanda ake zargin sun amsa laifukan da ake zarginsu a lokacin da ake gudanar da bincike.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Ibrahim Abdullahi ya yaba wa jami’an bisa yadda suke nuna ƙwarewa a duk lokacin da suke bakin aiki.

Ya kuma yi amfani da wannan dama inda ya buƙaci al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da bayar da haɗin kai ga jami’an tsaro musamman ta hanyar bayar da bayanai masu inganci domin magance tsaro a faɗin jihar.