✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum biyu sun shiga hannu da hodar iblis ta naira miliyan 264 a Abuja

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta samu nasarar cafke wasu mutum biyu dauke da hodar iblis mai nauyin fiye…

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta samu nasarar cafke wasu mutum biyu dauke da hodar iblis mai nauyin fiye da kilo daya a Abuja, babban birnin Najeriya.

Kwamandan hukumar reshen Abuja, Muhammad Malami Sokoto, ya ce an kama mutanen biyu ne da hodar wacce aka kiyasta kudinta ya kai naira miliyan 264.

A cewarsa, jami’an hukumar sun kama wani Emeka Okoro da hodar iblis mai nauyin giram 900 a cikin wata motar haya a kan titin Gwagwalada wanda yake shirin tafiya kasar Libya.

Ya ce, bayan tattara bayanan sirri da suka yi tun a ranar 26 ga watan Afrilu, sun samu nasarar kama Okoro ne a kan hanyar zuwa kasar Libiya inda zai ketara ta Jihar Kano da birnin Agadaz da kasar Nijar.

Emeka Okoro rike da tulin hodar iblis da aka kama shi da ita

 

Mista Okoro bayan shigarsa hannu, ya ce sun shafe tsawon watanni tara suna wannan harkalla ta safarar miyagun kwayoyi.

Kazalika, hukumar ta ce jami’anta sun kuma kama wani Ibrahim Bello da hodar mai nauyin giram 200 a yankin Zuba cikin birnin na Abuja.

Haka kuma, NDLEA a reshenta na Kogi, ta cafke wani mutum mai shekara 43, Cristian Godwin da kunshin tabar wiwi mai nauyin giram dubu 157.5 da aka boye a cikin wata mota kirar Peugeot J5 a Lokoja.