Rahotanni daga Kano sun bayyana cewa mutum biyu sun mutu bayan da suka fada rijiyoyi a wurare daban-daban a jihar.
Al’amarin ya faru a Kwagar Kanawa da ke Karamar Hukumar Gezawa da kuma Sabuwar Unguwa da ke Karamar Hukumar Rano.
- An zargi Kwamandan Hisbah da karkatar da kayan tallafin COVID19 a Kano
- Hatsarin mota ya lakume rayuka 11 a Kano da Kwara
- Satar yara a Kano: Kotu ta umarci a kamo wasu mutane
- Kano ta yi zarra wajen yaki da cin hanci a Najeriya —Ganduje
Hukumar Kashe Gobara ta jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda da ta ce ta samu kiran waya da misalin karfe 8 na safe daga Kwagar Kanawa.
Bayan isar jami’anta sun samu wata yarinya ce mai shekara tara Aisha Musa, ta fada rijiyar, wadda daga baya aka kai ta asibiti inda a nan ne ta rasu.
Bayan rasuwarta an damka gawarta a hannu mai unguwar Kwagar Kanawa Alhaji Abubakar Usman.
A wani lamarin mai kama da wannan, a Sabuwar Unguwa da ke Karamar Hukumar Rano, wani mutum, Isah Amadu Kamilu, mai shekara 65 ya fada rijiya kuma nan take ya mutu.
Shi ma dai jami’an kashe gobara sun damka gawarsa ga dan uwansa mai suna Malam Amadu Kamilu domin yi masa sutura.