Hukumar Kiyaye Haddurra ta Kasa (FRSC) ta ce hadurra 19,787 da mace-mace 9,227 aka samu a titunan Najeriya a tsakanin shekarar 2021 da 2022.
Shugaban Hukumar, Dauda Biu, ya ce alkaluman da hukumar ta tattara sun nuna daga watan Janiru zuwa Disambar 2021 hadurra 10,304 aka samu a fadin Najeriya.
A shekarar 2022 kuma an samu 9,483 wanda hakan ke nuna samun raguwar kashi takwas cikin 100 idan aka kwatanta da 2021.
Ya bayyana wa manema labarai ranar Litinin a Abuja cewa hukumar za ta jibge jami’ai 36,224 da kuma kayan aikin sintiri 1,226, domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa a lokacin bukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
“Wadannan hanyoyi sun hada da na Legas zuwa Ibadan, da Abuja zuwa Kano, da Nyanya zuwa Maraba, da sauran manyan hanyoyi,“ in ji shi.