✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 9 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

Bakwai daga cikin wadanda suka mutu mata ne, biyu kuma maza.

Akalla mutum tara ne aka tabbatar da rasuwarsu, wani mutum daya kuma ya jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Karamar Hukumar Birniwa ta Jihar Jigawa.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar ‘Golf 3 saloon’ da wani babur din acaba a ranar Juma’a.

Wani ganau ya ce hatsarin ya faru ne ranar Juma’a a kusa da garin na Birniwa da ke kan hanyar zuwa Nguru na Nijar Yobe.

Majiyar ta ce motar ce ta kwace wa direbanta, inda ta je ya doki dan acabar sakamakon gudun wuce sa’ar da take yi.

Kakakin Hukumar tsaro ta Sibil Defens (NSCDC) a Jihar, Adamu Shehu, shi ma ya tabbatar wa wakilin Aminiya faruwar hatsarin ranar Asabar a Dutse, babban birnin Jihar.

Adamu ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin mota kirar Golf mai lamba CZ865RBC da kuma babur din mai lamba 827NGR.

Kakakin ya ce nan take aka tabbatar da rasuwar mutum tara; bakwai mata daya kuma namiji guda, sai kuma wani mutum daya da ya jikkata.

Ya ce tuni aka garzaya da mamatan zuwa babban asibitin garin Birniwa, inda a can aka tabbatar da rasuwarsu.

Kakakin na NSCDC ya kuma ce tuni aka mika dukkan gawarwakin mutum taran ga iyalansu, kuma tuni aka yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.