Akalla mutum 82,302 ke fama da cuta mai karya garkuwar jiki da aka fi sani da Kanjamau ko Sida a Jihar Nasarawa.
Shugabar Sashen Dakile Yaduwar Cutar Kanjamau a Ma’aikatar Lafiyar jihar, Halimatu Musa ce ta bayyana hakan yayin wani taron kwanaki biyu na horas da gidajen jaridu kan yaki da cutar Sida musamman a tsakanin matasa.
- Dalilin da babu ranar dawo da jigilar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna —Ministan Sufuri
- Kannywood ta yi martani kan hana amfani da kakin ’yan sanda a fim
Aminiya ta ruwaito cewa, an gudanar da taron ne a Abuja tare da hadin gwiwar Cibiyar Kula da Yaduwar Cutar Kanjamau ta Kasa (NASACA).
Da take bayyana cewa kashi 90 cikin 100 na masu fama da cutar a jihar suna kokarin dakile tasirin kwayar cutar a jikinsu, sai dai ta kuma shawarci wadanda abin ya shafa da su yi riko da shan magani ka’in-da-na’in.
Yayin da take neman karin taimako daga Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da sauran abokan hadin gwiwa don samarwa da kuma wadata jihar da kayayyakin gwaji da sauran matakan da suka dace don dakile yaduwar cutar a jihar, Hajiya Halimatu ta bukaci jama’a da su rika bincikar lafiyarsu daga lokaci zuwa lokaci.
A nata jawabin, Babbar Daraktar NASACA reshen Jihar Nasarawa, Dokta Ruth Bello, ta ce an yi wa gidajen jaridu wannan horo ne domin sanar da su nasarorin da aka samu da kuma matakan da aka tanada domin yaki da wannan annoba ta cutar Sida a fadin jihar.
A cewarta, an samu raguwar yaduwar cutar Kanjamau daga kashi 6.4 zuwa 2.0 cikin dari a fadin jihar a sakamakon agajin da kafofin watsa labarai ke bai wa Cibiyar NASACA wajen inganta hanyoyin wayar da kan al’umma game da musibar da ke tattare da cutar.
Ta yi kira ga gidajen jaridu a kan kada su yi kasa a gwiwa a kokarin da suke yi na fadakarwa da kuma wayar da kan al’umma game da cutar.
Dokta Bello ta bukaci kafafen yada labaran da su yi amfani da salon watsa rahotanni na gaskiya, wanda zai taimaka wajen kiyaye lafiya da tallafa wa wadanda suka kamu da cutar a cikin al’umma, musamman mata da matasa.
Babbar Daraktar ta gargadi ’yan jarida kan illar da ke tattare da yada rahotannin da basu dace ba a kan cutar kanjamau, inda ta yi kira da su rika amfani da kalmomi da harsunan da za su kara wa masu dauke da kwayar cutar kwarin gwiwa.