Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, ta kama wasu mutum takwas da ake zargi da hannu a kisan wasu jami’anta a yankin Ughelli da ke Jihar Delta.
Kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Abuja.
- Netanyahu ya amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
- Masu fasa kwauri na ɗaukar hayar ’yan daba su kai mana hari – Kwastam
Ya ce jami’an na bakin aiki a ranar 23 ga watan Fabrairu lokacin da wasu suka kai musu hari, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’anta shida.
Adejobi, ya ce kamen ya biyo bayan wani bincike da ’yan sandan suka gudanar a yankin.
A cewarsa, mutum biyar aka fara kamawa bayan faruwar lamarin, yayin da aka kama karin wasu mutu uku a wurare daban-daban.
Ya ce kamen ragowar mutum ukun, ya biyo bayan hadin kan mutanen da aka fara kamawa.
Adejobi, ya ce a halin yanzu wadanda ake zargin suna hannu, kuma rundunar na ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
Ya ce rundunar ’yan sandan Najeriya ta himmatu wajen kama masu aikata laifin kisan kai da sauran laifuka don gurfanar da su a gaban kuliya.
Kakakin ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, da zarar sun kammala bincike.
A cewarsa rundunar ta yi bakin cikin yadda aka hallaka jami’anta da ke bakin yi wa al’umma hidima.
“Muna jajanta wa iyalan jami’an da suka mutu a wannan danyen aikin.
“Muna so mu sake jaddada cewa wadanda suka kashe jami’anmu ba za su tsira ba sai an hukunta su,” in ji shi.
A ranar 23 zuwa 26 ga watan Fabrairu aka kashe jami’an ’yan sandan a yankin Ughelli, yayin da wasu shida suka bace.