Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta damƙe wasu mutum takwas da ake zargi da hannu a kisan wani malami a Jami’ar Maiduguri (UNIMAID), Dokta Abdulkadir Kamal.
Wasu da ba a san ko su wane ne ba, suka yi wa malamin kisan gilla a ofishinsa da ke Jami’ar a ranar Lahadi.
- Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Senegal
- Limamin Juma’a Ya Yi Murabus Kan Kyautar Kuɗi
An tsinci gawar malamin dauke da raunin wuka a wasu sassan jikinsa.
Bayan kashe malamin, an yi awon gaba da wasu kayayyaki masu amfani a cikin motarsa.
Har yanzu iyalansa ko Jami’ar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da kisan malamin ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Kenneth ya ce tuni aka cafke mutum takwas da ake zargi da hannu a kisan malamin.
A cewarsa rundunar ta samu rahoton kisan malamin a ofishinsa, sannan wadanda suka yi aika-aikar sun sace motarsa.
Kakakin ya ce rundunar na ci gaba da gudanar da bincike, kuma da zarar ta samu karin bayani za ta sanar da al’ummar jihar abin da ake ciki.