✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 8 sun mutu, 36 sun ji rauni bayan tirela ta fado daga gadar sama

Rahotanni sun ce motar wacce take dauke da manja da mutane 61 a cikinta ta kwacewa direbanta ne sannan ta fado daga gadar

Akalla mutum takwas ne suka mutu a kan babbar hanyar Oshogbo zuwa Ibadan dake jihar Osun a ranar Asabar bayan wata babbar motar tirela ta fado daga gadar sama.

Rahotanni sun ce motar wacce take dauke da manja da mutane 61 a cikinta ta kwacewa direbanta ne sannan ta fado daga gadar, lamarin da kuma ya yi sanadin raunata karin wasu mutum 36.

Jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) a jihar da na ’yan sanda da kuma na kwana-kwana sun ziyarci wurin bayan faruwar lamarin domin ceto mutane.

Kwamandar shiyya ta hukumar FRSC a jihar, Kudirat Ibrahim ta tabbatarwa da Aminiya faruwar lamarin tare da mika ta’aziyyarta ga iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su.

Da take magana ta bakin kakakin hukumar, Agnes Ogungbemi, kwamandar ta ce tirelar kirar Volvo mai lambar KMC35ZJ ta fado ne daga kan gadar da baya, sannan jarkunan manjan dake cikinta suka rika fadowa kan mutanen dake cikin motar tare da kashe takwas daga cikinsu.

Tuni dai akai garzaya da wadanda suka ji raunukan zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Osun da kuma asibitin jihar dake Asubiaro a birnin Oshogbo, yayin da mamatan kuma aka wuce da su dakin adana gawawwaki.