✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 8 cikin kowanne 10 a China na dauke da COVID-19 – Rahoto

Gwamnati ta ce akwai yiwuwar cutar ta sake dawowa a 'yan watanni masu zuwa

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta kasar China ta ce akwai yiwuwar kimanin kaso 80 cikin 100 na al’ummar kasar sun kamu da cutar COVID-19.

Hakan dai a cewar hukumar na nuni da cewar cutar za ta iya sake dawowa kasar ka’in da na’in a ’yan watanni masu zuwa.

Wani masani a hukumar, Wu Zunyou ne ya bayyana hakan ranar Asabar, inda ya ce hakan ba zai rasa nasaba da yadda aka kyale mutane suka yi ta tafiye-tafiye yayin bikin sabuwar shekarar Lunar ta kasar da ake yi a karshen makon nan ba.

Dandalin sada zumunta na Weibo ya ambato Wu na cewa sabbin nau’ukan cutar na Omicron ne ke ci gaba da yaduwa, inda ya ce, “yanzu haka sun kama kaso 80 cikin 100 na al’ummar kasar.”

Sanarwar ta Mista Wu na zuwa ne a daidai lokacin da miliyoyin daruruwan ’yan kasar ke tafiye-tafiye a fadin kasar saboda hutun sabuwar shekarar, wanda a shekarun baya aka dakatar saboda barazanar cutar.

Ana dai fargabar yawan tafiye-tafiyen na iya ta’azzara yaduwar cutar musamman a yankunan karkara da ke da karancin kayan dakile yaduwarta da yawa a lokaci guda.

Ya zuwa ranar 12 ga watan Janairu, kusan mutum 60,000 ne suka mutu sanadiyyar cutar, kamar yadda alkaluman gwamnati suka nuna.

Sai dai wasu kwararru na da ra’ayin cewar akwai yiwuwar yawan mutanen ma ya wuce adadin, saboda akwai mutane da dama da suka mutu a gida, kuma likitoci da dama sun ce ba sa samun kwarin gwiwar ayyana cutar a matsayin dalilin mutuwar wasu mutanen.