✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 7 ’yan gida daya sun rasu bayan cin Dambu mai guba a Zamfara

Sun rasu ne bayan cin dambu mai guba

Mutum bakwai ’yan gida daya sun rasu a kauyen Danbaza da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, bayan cin gurbataccen abinci.

Aminiya ta gano cewa lamarin ya faru ne sakamakon yin amfani da wasu ganyakai da ke dauke da guba don yin dambu.

Daga cikin mutanen da abin ya shafa biyu mata ne, sai kananan yara su biyar.

Wani dan uwan iyalan da lamarin ya shafa, Muhammad Kabir, ya ce jim kadan da kammala cin dambun, nan take mutum hudu suka mutu, yayin da ragowar ukun kuma aka garzaya da su asibiti.

Muhammad ya kuma ce su ma ragowar mutum ukun da suka rasu duka an yi musu jana’iza.

Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta jihar, SP Muhammed Shehu ya ce ba shi da masaniya a kai.

Sai dai ya ce zai bincika daga baturen ’yan sanda (DPO) na Maradun.