✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 7 sun rasu bayan rushewar gini a Jigawa

Mutum bakwai sun rasu nan take, daya ya jikkata sakamakon rushewar ginin kasa a Karamar Hukumar Birniwa

Wasu mutum bakwai sun rasu a safiyar Asabar sakamakon rushewar gini a Karamar Hukumar Birniwa ta Jihar Jigawa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jiagawa ta ce mutanen sun rasu ne nan take bayan ginin ya rufta a kansu da misalin karfe 5:47 na asuba a kauyen Bursali.

Kakakin Rundunar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya kara da cewa wani mutum daya ya jikkata sakamakon rushewar ginin.

Ya ce ’yan sanda sun garzaya da su zuwa Babban Asibitin Birniwa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwar mutum bakwai din, na takwas din kuma yake samun kulawa.

Ya kuma bayyana cewa ginin da ya yi ajalin mutanen an yi shi ne da kasa.