✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 7 sun mutu a hatsari bayan kamfe din Tinubu a Kano

Mutane bakwai sun rasu ne a kan hanyarsu ta komawa gida bayan halartar taron yakin neman zaben Tinubu.

Wasu mutum bakwai sun mutu a wani hatsarin mota bayan halartar taron yakin neman zaben Tinubu da aka yi a Jihar Kano.

Wani ganau, ya ce mamatan ’yan garin Kwanar Dangora ne, kuma sun rasu ne bayan wata mota kirar Golf ta yi karo da wata tirela a kan Babbar Hanyar Kano- Zariya da misalin karfe 6 na yamma ranar Laraba.

Tukur Lawan, daya daga cikin wadanda suka halarci taron siyasar, ya ce “Dukkaninmu mun halarci taron, muna kan hanyarmu ne wannan mummunan abu ya faru, yau mun wayi gari cikin bakin ciki.

“Bayan motocin sun yi karo, tirelar ta murkushe Golf din ta hada ta da ginin da ke gefen hanya.”

Ya ce a take mutum biyar suka mutu, ragowar biyun kuma sun rasu ne a Asibitin Kwararru na Murtal Mohammed da ke Kano.

Shi ma wani mazaunin yankin, mai suna Mahmud Abubakar Kiru, ya ce mutane sun kadu da rasuwar mutanen ciki har da ’yan siyasar da suka halarci jana’izar mamatan.

Ya ce Sanata Kabiru Gaya, ya halarci jana’izar mamatan wadanda dukkansu ’yan kwanar Dangora ne.

Da aka tuntubi kakakin Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) na jihar, Abdullahi A. Labaran, ya ce har yanzu ba su samu labarin faruwar hatsarin ba.