✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 7 sun mutu, 31 sun jikkata a hatsarin tirela a Gombe

Mutum bakwai sun rasu wasu 31 suna kwance a asibiti bayan hatsarin wata tirela a Jihar Gombe

Mutum 7 ne aka tabbatar sun mutu wasu 31 kuma sun samu raunuka a wani haɗarin mota a kan hanyar Kaltungo zuwa Cham da ke Jihar Gombe.

Kwamandar Hukumar Kiyaye Haɗura ta Jihar, Ƙaura ta ce hatsarin ya auku ne sakamakon tsinkewar burkin wata babbar motar lemon kwalba.

Ta ce mutum 38 — maza 34, mata biyu da ƙananan yara biyu, ne suke cikin babbar motar a lokacin da hatsarin ya auku da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Kwamanda Ƙaura ta kara da cewa, maza biyar da mace ɗaya da ƙaramin yaro ɗaya ne hatsari ya yi ajalinsu, ragowar mutum 31 kuma ana jinyar su a asibiti.

Ta ce an ajiye gawarwakin a Babban Asibitin Kaltungo inda ake kula da lafiyar waɗanda suka samu raunuka a hatsarin.

Ƙaura ta gargaɗi matafiya da su guji shiga tireloli don neman sauƙin kuɗin mota, tana mai jam hankalinsu kan hatsarin da ke tattare da hakan.

Ta ce “Ba a yi tirela don ɗaukar fasinja ba, ya kamata matafiya su riƙa kiyaye tare da la’akari da munin hatsarin motocin. Ga shi hatsari ɗaya aka yi amma sai da muka kwashe yini guda muna aiki a kai.”

Kazalika ta ja hankalin direbobi da su riƙa tabbatar da lafiyar ababen hawansu a kodayaushe.