✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akalla mutum 820 sun rasu a girgizar kasa a Morocco

Kasashen duniya na mika sakon jajensu ga al'ummar kasar Morocco kan girgizar kasa da ta hallaka daruruwan mutane

Kasashen duniya na mika sakon jajensu ga al’ummar kasar Morocco bayan girgizar kasa da ta kashen mutane sama da 820, wanda kwararru suka ce shekara 120 rabon da samu girgizar kasar irinsa a yankin.

Gwamnatocin kasashen Gabas da Tsakiya, Amurka, China, Turkiyya, Rasha, Ukraine, Pakistan da kungiyoyin kasa da kasa irinsu ECOWAS da EU da tarayyar Afirka (AU) sun aike wa gwamnati da al’ummar Morocco sakonnin jaje kan girginsar kasar mai karfin maki 6.8.

Hukumomin kasar Morocco sun sanar da cewa yawan wadanda suka rasu a girgizar kasar ta daren Juma’a yana takaruwa.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta ce wasu akalla 672 sun samu raunuka, 205 daga cikinsu kuma na cikin mawuyacin hali.

Ma’aikatar ta tabbatar ta ce girgizar kasar mai karfin maki 6.8 ta yi barna a yankunan Al-Haouz, Marrakesh, Ouarzazate, Azilal, Chichaoua da kuma Taroudant.

A yayin da ake ci gaba da aikin ceto bayan aukuwar iftila’in, jama’a tser daga gidajensu tun a cikin dare domin kubutar da rayuwarsu.

Grigizar kasa Morocco
AL’ummar Morocco sun koma yi kaura zuwa wani dandali a binin Marrakesh bayan girgizar kasa mai karfin maki 6.8 da ta kasu mutum kusan 300 a daren 8 ga Satumba, 2023. (Hoto: Fadel Senna/ AFP).

Girgizar kasar mai karfin maki 6.8 ta auku ne na kusan minti 10 a Marrakesh, yankin da masu  yawon bude ido ke yawan ziyarta kuma an ji motsa a biranen Rabat, Casablanca da kuma Essaouira.

Wani mazaunin Marrakesh mai shekaru 33, Abdelhak El Amrani, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa girgizar kasar ta rika walagigi da gine-gine.

“Da na ga yadda gine-gine suke motsawa sai na fahimci cewa girgizar kasa aka samu, shi ne na yi maza muka fita waje, muka samu mutane sun fiffito, kowa a firgice,  kananan yara na ta kuka.

“An dauke wutar lantarki da layin sadarwa, amma daga bisani sun dawo, ko da yake kowa na waje har yanzu,” in ji shi.