Kasashen duniya na mika sakon jajensu ga al’ummar kasar Morocco bayan girgizar kasa da ta kashen mutane sama da 820, wanda kwararru suka ce shekara 120 rabon da samu girgizar kasar irinsa a yankin.
Gwamnatocin kasashen Gabas da Tsakiya, Amurka, China, Turkiyya, Rasha, Ukraine, Pakistan da kungiyoyin kasa da kasa irinsu ECOWAS da EU da tarayyar Afirka (AU) sun aike wa gwamnati da al’ummar Morocco sakonnin jaje kan girginsar kasar mai karfin maki 6.8.
Hukumomin kasar Morocco sun sanar da cewa yawan wadanda suka rasu a girgizar kasar ta daren Juma’a yana takaruwa.
Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta ce wasu akalla 672 sun samu raunuka, 205 daga cikinsu kuma na cikin mawuyacin hali.
- ’Yan kungiyar asiri sun fille kan DPO a Ribas
- Shinkafa ta yi tsadar da ba a taɓa gani ba cikin shekara 15 a duniya — FOA
Ma’aikatar ta tabbatar ta ce girgizar kasar mai karfin maki 6.8 ta yi barna a yankunan Al-Haouz, Marrakesh, Ouarzazate, Azilal, Chichaoua da kuma Taroudant.
A yayin da ake ci gaba da aikin ceto bayan aukuwar iftila’in, jama’a tser daga gidajensu tun a cikin dare domin kubutar da rayuwarsu.
Girgizar kasar mai karfin maki 6.8 ta auku ne na kusan minti 10 a Marrakesh, yankin da masu yawon bude ido ke yawan ziyarta kuma an ji motsa a biranen Rabat, Casablanca da kuma Essaouira.
Wani mazaunin Marrakesh mai shekaru 33, Abdelhak El Amrani, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa girgizar kasar ta rika walagigi da gine-gine.
“Da na ga yadda gine-gine suke motsawa sai na fahimci cewa girgizar kasa aka samu, shi ne na yi maza muka fita waje, muka samu mutane sun fiffito, kowa a firgice, kananan yara na ta kuka.
“An dauke wutar lantarki da layin sadarwa, amma daga bisani sun dawo, ko da yake kowa na waje har yanzu,” in ji shi.