Akalla mutum 60 ne ake fargabar sun mutu sakamakon fashewar wata motar daukar gas a kasar Haiti.
Mataimakin Magajin Garin birnin Cap-Haitien, Patrick Almonor, wanda ya ziyarci inda lamarin ya faru, ya ce ya ga gawar akalla mutum 60 da suka rasu a sakamakon ibtila’in.
- Tambayoyi 10 da Shugaba Buhari zai amsa da kansa
- Birtaniya ta cire Najeriya a jerin kasashe masu yada COVID-19
Sai dai Fira Ministan kasar, Ariel Henry, ya ce mutum 40 ne aka tabbatar sun mutu.
Rahotanni na nuni da cewa motar ta fadi ne a lokacin da take kokarin na kauce wa wani babur din haya.
Almonor ya ce hatsarin ya yi muni sosai ta yadda ba zai iya tantance adadin mutane da suka kone ba, sakamakon bindiga da motar ta yi.
Rahotanni sun ce faduwar motar ta sa manta ya rika malala a kan titi, wanda hakan ya sa mutane mamaye wurin domin dibar man, daga bisani kuma wuta ta tashi.
Magajin Garin ya ce, akalla gidaje 20 da ke kusa da inda wutar ta shi ne suka kone kurmus, amma har yanzu ba san adadin wanda suka ji rauni ba.
Wata ma’aikaciyar lafiya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Justinien, ta bayyana cewa ba su da isassun ma’aikatan da za su iya kula da wadanda suka samu raunuka.
Fira Ministan kasar ya bayar da hutun kwana uku don gudanar da zaman makokin wadanda suka rasa rayukansu a sanadin hatsarin.