Kwana biyu bayan wani hatsarin mota ya yi ajalin mutum 14 a Kafin Hausa a Jihar Jigawa, wani sabon hatsari ya yi sanadin mutuwar mutum shida.
Hatsarin ya faru ne da daren Talata, a kan titin Auyo-Adiyani da ke Ƙaramar Hukumar Guri.
- Sojoji sun kama ƙasurguman ’yan bindiga 2, sun ƙwato alburusai a Filato
- Babban layin lantarkin Najeriya ya faɗi karo na 12 a 2024
Majiyoyi sun ce waɗanda suka rasu a hatsarin ’yan uwan juna ne daga garin Adiyani, bayan dawowa daga ta’aziyya.
Ganau, sun ce al’ummar yankin har yanzu suna jimamin hatsarin farko, yayin da wannan sabon hatsarin ya sake jefa su cikin baƙin ciki.
Adadin mutanen da suka mutu a baya-bayan sun kai mutum 20, lamarin da ya ƙara haifar da damuwa kan tsaro a kan tituna a yankin.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, DSP Shi’isu Lawan Adam, ya tabbatar da aukuwar hatsarin.
Ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin faruwar hatsarin.