✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 1,000 na neman mafaka a ofishin ’yan sanda bayan fadan kabilanci

Ana zargin kabilar Kimyal da kashe wani dan siyasa daga kabilar Yali.

Hukumar ’yan sanda a Kasar Indonesia ta tabbatar da mutuwar mutum shida tare jikkata wasu 41 a wani fadan kabilanci da ya barke a lardin Papua na kasar.

Kakakin ’Yan Sandan Lardin Papua, Ahmad Musthofa Kamal, ya tabbatar da faruwar rikicin tsakanin kabilar Kimyal wadanda suka farmaki kabilar Yali a yankin Yahukimo a ranar Lahadi.

“Har zuwa yanzu babu tabbacin abin da ya jawo rikicin, amma akalla mutum 1,000 ne suka kai kansu ofishin ’yan sanda don neman dauki,”  a cewar Kamal.

Sai dai wasu kafafen yada labarai a kasar sun rawaito cewa wani dan siyasa da aka ce ciwon zuciya ne ya yi ajalinsa, kabilar Kimyal, ne suka kashe shi.

Lardin Papua, wuri ne da ya yi kaurin suna wajen rashin zaman lafiya a kasar tun shekarar 1960.