Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi, ta sanar da rasuwar mutane shida, yayin da wasu 54 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya ritsa da su.
Kwamandan Hukumar na jihar, Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da afkuwar hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.
- Bana shakkar faduwa zabe a 2023 – Makinde
- Mahara sun kashe matashi, sun dauke mahaifiyarsa a Jigawa
- ’Yan bindiga: Sheikh Gumi yana mana katsalandan – Masari
- Ba sace ni aka yi ba, guduwa na yi – Amaryar Kano
Ya sanar da cewa da misalin karfe 11:26 na safiyar ranar Laraba ne hadarin ya ritsa da wasu ‘yan kasuwa da suka taso daga garin Darazo da ke jihar zuwa kasuwar Dakuku a jihar Gombe.
Abdullahi, ya kara da cewar bincikensu ya gano musu cewar gudun wuce kima ne ya haddasa hadarin.
A cewarsa, “Motar da ke dauke da fasinjoji 72, shida daga cikinsu sun riga mu gidan gaskiya, sai kuma ragowar 54 da suka ji raunuka daban-daban, wanda tuni aka garzaya da su babban asibitin garin Darazo, don ba su kulawar da ta dace.”
Kwamandan ya gargadi masu ababen hawa da su guji yin gudun wuce sa’a da kuma tukin ganganci.