✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 6 sun mutu, 11 sun jikkata a hatsarin mota

Mutum shida ne suka mutu wasu 11 kuma suka ji rauni a wani hatsari da ya rutsa da motar bus da wata tirela. Rahotanni sun…

Mutum shida ne suka mutu wasu 11 kuma suka ji rauni a wani hatsari da ya rutsa da motar bus da wata tirela.

Rahotanni sun ce motocin biyu sun yi taho mu gama ne a hanyar Nteje-Onitsha a Jihar Anambra ranar Lahadi.

Shaidu sun ce an kai gawarwakin wadanda suka mutun dakin ajiye gawa na asibitin Iyi-Ene, Ogidi, inda ake kula da wadanda suka samu rauni.

Kakakin Kwamandan Hukumar Kare Hadura ta Kasa (FRSC) na jihar, Kamal Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin.