✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 6 sun jikkata, an ƙone kayayyaki a rikicin fili a Neja

Rundunar 'yan sandan jihar ta cafke mutum biyu da ake zargi da haddasa rikicin.

Aƙalla mutum shida ne suka jikkata, yayin da kuma aka ƙone tarakta, babur, da wasu kayayyaki sakamakon rikicin filaye guda biyu a Jihar Neja.

Rikicin ya samo asali ne tsakanin al’ummar Dakumi da Gbage da kuma ƙauyukan Katakpa da Elegi a Ƙaramar Hukumar Lapai.

An jikkata mutum biyu a rikicin Dakumi da Gbage, yayin da aka jikkata mutum huɗu a rikicin Katakpa da Elegi.

Sai dai daga bisani an garzaya kotu sakamakon mummunan tashin hankali da aka samu kan rikicin.

Mazauna garin sun bayyana cewa an kai mutum huɗu daga cikin waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibiti na Gulu.

Sun roƙi gwamnati da ’yan sanda su shiga tsakani kafin rikicin ya haifar da mummunan sakamako.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce an kama mutum biyu, sannan ana ƙoƙarin kama sauran waɗanda suka haddasa rikicin.